Rundunar Sojin Iran ta sanar da kulle mashigar Hormuz inda jiragen dakon man fetur ke wucewa.

Rundunar Sojin Iran ta sanar da kulle mashigar Hormuz inda jiragen dakon man fetur ke wucewa.

Rundunar juyin juya halin Musuluncin ta Iran, IRGC ta sanar da cewa Mashigar Tekun Hormuz na ƙarƙashin cikakken ikon ƙasar ta Iran, a daidai lokacin da rikicin siyasa da na soja ke ƙara kamari tsakanin Iran da Amurka tare da kawayenta.

IRGC ta bayyana cewa tana da cikakkiyar damar sa ido da kuma iko kan dukkanin zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar, wadda ke ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin safarar man fetur a duniya, inda kusan kashi 20 cikin 100 na man fetur na duniya ke bi ta nan.

Sanarwar ta zo ne bayan barazanar da shugaban Amurka ya yi na ɗaukar matakan soji don tabbatar da ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa, musamman na tankokin mai. 
Sai dai Iran ta ce duk wata barazana ko matsin lamba ba zai sa ta ja da baya ba, tana mai jaddada cewa tsaron yankinta da muradun ƙasarta ba abin sassauci ba ne.

A martaninta, Iran ta gargadi cewa duk wani yunƙurin kutsawa ko rakiyar jiragen ruwa da karfi zai iya janyo mummunan rikici a yankin, tare da illar da ka iya shafar tattalin arzikin duniya, musamman kasuwannin makamashi.

Masana harkokin tsaro da tattalin arziki sun ce wannan yanayi na iya haifar da hauhawar farashin mai a duniya, yayin da kamfanonin jiragen ruwa ke fuskantar barazanar tsaro da ƙarin kuɗin inshora.

Rikicin dai na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a Gabas ta Tsakiya, lamarin da ke ƙara tsananta fargabar barkewar faɗa mai faɗi tsakanin manyan ƙasashe.

News Translation in English Language.

Iran Says It Has Full Control of the Strait of Hormuz, Warns Against Oil Tanker Escort.

Iran’s Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) has announced that the Strait of Hormuz is under its complete control, amid escalating political and military tensions between Iran and the United States and its allies.

In a statement issued on Tuesday, the IRGC said it has full surveillance and operational dominance over all maritime traffic passing through the strait, one of the world’s most critical energy routes. About 20 percent of global crude oil shipments transit the narrow waterway linking the Persian Gulf to international markets.

The declaration follows warnings from US officials about taking military measures to guarantee freedom of navigation, including the possible escort of oil tankers. Iran, however, said it would not retreat in the face of pressure, stressing that the defense of its sovereignty and national interests is non-negotiable.

Iranian officials cautioned that any attempt to forcibly escort vessels or challenge Tehran’s control could trigger serious regional confrontation, with far-reaching consequences for global energy security and international trade.

Security and economic analysts say the rising tensions could push global oil prices higher, as shipping companies face increased security risks and soaring insurance costs.

The standoff comes as instability continues to spread across the Middle East, intensifying fears of a wider conflict involving major world powers.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form