Rahotanni daga Al Jazeera sun nuna cewa rikicin da ke gudana tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran tun ranar 28 ga Fabrairu, 2026, ya kawo tashin farashin man fetur a kasashe da dama na duniya.
A kalla kasashe 85 ne suka fuskanci karuwar farashin man fetur tun bayan barkewar rikicin.
Vietnam na fama da mafi girman tashin farashin, inda farashin man fetur ya karu da kusan 50 % cikin kankanin lokaci.
Sauran kasashen da suka samu karin farashin mai tsanani sun hada da Kasar Laos (≈33 %) da Kambodiya (≈19 %) da Ostiraliya (≈18 %), da Amurka (≈17 %).
Babban abin da ya janyo wannan tashin farashin shi ne matsalolin samar da man fetur da rikicin ya haifar, musamman a hanyar mashigar Hormuz, wadda take daya daga cikin manyan hanyoyin fitar da mai na duniya.
Masu sharhi sun bayyana cewa rikicin zai iya ci gaba da yin tasiri kan farashin makamashi a duniya har zuwa lokacin da za a samu daidaituwa a kasuwannin man fetur.
News Translation in English Language.
Global Fuel Prices Surge in Several Countries Amid U.S.–Israel–Iran Tensions.
Reports from Al Jazeera indicate that the ongoing conflict involving United States, Israel, and Iran since February 28, 2026, has triggered a sharp rise in fuel prices in many countries around the world.
At least 85 countries have reportedly experienced increases in petrol prices since the outbreak of the crisis.
Vietnam has recorded the highest surge, with petrol prices rising by nearly 50 percent within a short period. Other countries experiencing significant increases include Laos (about 33 percent), Cambodia (around 19 percent), Australia (approximately 18 percent), and the United States (around 17 percent).
Analysts say the sharp increase is largely driven by disruptions in global oil supply caused by the conflict, particularly around the Strait of Hormuz, one of the world’s most critical routes for crude oil shipments.
Experts warn that the crisis could continue to affect global energy prices until stability returns to the international oil market.
Tags
Labarai
