Uwargidan Gwamnan Jihar Yobe State, Hajiya Hafsat Mai Mala Buni, ta raba kayan abinci ga mata 2,000 marasa galihu a fadin jihar domin tallafa musu a wannan wata mai alfarma na Ramadan.
Shirin rabon kayan abincin na daga cikin kokarin tallafa wa mata masu rauni da kuma rage musu radadin halin da ake ciki na tsadar rayuwa a lokacin azumi.
An ce an gudanar da rabon kayan ne a karkashin shirin Renewed Hope Initiative, inda aka bai wa mata daga kananan hukumomi 17 na jihar tallafin kayayyakin abinci domin su samu saukin gudanar da ibadun watan Ramadan.
Uwargidan gwamnan ta samu wakilcin Kwamishinar Jin Kai da Kula da Bala’o’i ta jihar, Hajiya Mairo Amshi, wadda ta bayyana cewa shirin na da nufin karfafa jin kai da taimakon juna a tsakanin al’umma, musamman ga marasa karfi.
Kayayyakin da aka raba sun hada da shinkafa da taliya (spaghetti) da man girki, domin taimaka wa zawarawa da sauran mata marasa galihu su samu abin da za su ci a lokacin azumi.
A nata bangaren, Kwamishinar Harkokin Mata ta jihar, Hajiya Yajalo Badama, ta yaba da wannan shiri, tana mai cewa ya yi daidai da manufofin gwamnatin Gwamnan jihar, Mai Mala Buni, na tallafa wa talakawa da inganta rayuwar al’umma.
Ta kara da cewa irin wadannan shirye-shirye na taimakawa wajen karfafa hadin kai da tausayi a tsakanin jama’a, musamman a wannan lokaci na Ramadan da Musulmi ke mayar da hankali kan ibada da ayyukan alheri.
Tags
Labarai
