Gwamnan Kano Ya Sallami Shugaban Ma’aikatan Jihar.


Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sallami Shugaban Ma’aikatan Jihar, Alhaji Abdullahi Musa, daga mukaminsa nan take.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Tofa, ya fitar, ya bayyana cewa matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na sake fasalin aikin gwamnati a jihar domin inganta aiki da ƙarfafa ladabtarwa da kuma tabbatar da kyakkyawan gudanar da ayyukan gwamnati.

Sanarwar ta kuma ce gwamnan ya gode wa tsohon Shugaban Ma’aikatan Jihar bisa gudunmawar da ya bayar yayin da yake kan mukaminsa, tare da yi masa fatan alheri a rayuwarsa ta gaba.

A halin yanzu, an umarci Hajiya Bilkisu Shehu Maimota, wadda ke rike da mukamin Sakatare na dindindin a sashen Gudanarwa da Harkokin Gabaɗaya na Ofishin Majalisar Zartarwa ta Jihar, da ta riƙe mukamin Shugaban Ma’aikatan Jihar na rikon ƙwarya har sai an naɗa wanda zai maye gurbin a hukumance.

Har ila yau, gwamnan ya umarci Abdullahi Musa da ya miƙa ragamar ofishin ga mai riƙon muƙamin nan take.

News Translation in English Language.

Kano Governor Sacks Head of Service.

The Governor of Kano State, Abba Kabir Yusuf, has dismissed the State Head of Service, Abdullahi Musa, from office with immediate effect.

This was contained in a statement issued by the governor’s spokesperson, Sanusi Bature Tofa, who said the decision was part of the administration’s efforts to reposition the state civil service for greater efficiency, discipline, and improved service delivery.

According to the statement, the governor appreciated the outgoing Head of Service for his contributions and service to the state during his tenure, wishing him success in his future endeavours.

Following the development, Hajiya Bilkisu Shehu Maimota, the Permanent Secretary for Administration and General Services at the Cabinet Office, has been directed to serve as Acting Head of Service pending the appointment of a substantive replacement.

The governor also instructed Abdullahi Musa to hand over the affairs of the office to the acting Head of Service with immediate effect.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form