Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo murnar cika shekara 89 a duniya, yana mai yabawa da irin tasirin da ya yi wajen gina Najeriya da nahiyar Afirka.
A cikin saƙon taya murnar da ya fitar, Tinubu ya bayyana Obasanjo a matsayin jagora mai gagarumar kwarewa da tasiri, wanda ya taka muhimmiyar rawa a tarihin siyasar Najeriya.
Shugaban ƙasar ya tuna cewa Obasanjo ya taɓa zama shugaban mulkin soja na Najeriya daga shekarar 1976 zuwa 1979, inda ya mika mulki ga farar hula, sannan daga baya ya sake zama shugaban ƙasa a gwamnatin dimokuraɗiyya daga 1999 zuwa 2007.
Tinubu ya kuma jaddada irin jarumtar da tsohon shugaban ya nuna a lokacin yaƙin basasa na Najeriya, da kuma irin gwagwarmayar da ya sha har da ɗaurin kurkuku saboda tsayawa kan gaskiya da adalci.
Ya kara da cewa Obasanjo ya ci gaba da ba da gudummawa wajen ci gaban ƙasa ta hanyar shawarwari da rubuce-rubuce da kuma tsoma baki kan manyan batutuwan ƙasa.
Tinubu ya yi addu’ar Allah ya ƙara wa tsohon shugaban lafiya da ƙarfi da hikima domin ya ci gaba da hidimtawa Najeriya da bil’adama baki ɗaya.
News Translation in English Language.
Tinubu Celebrates Obasanjo’s Monumental Influence on His 89th Birthday.
Nigerian President Bola Ahmed Tinubu has congratulated former President Olusegun Obasanjo on his 89th birthday, praising his enduring influence on Nigeria and the African continent.
In a statement marking the occasion, Tinubu described Obasanjo as a seasoned and impactful leader who has played a pivotal role in Nigeria’s political history.
He recalled Obasanjo’s tenure as a military head of state from 1976 to 1979, during which he handed over power to a civilian government, and later as a democratically elected president from 1999 to 2007.
Tinubu also highlighted Obasanjo’s courage during Nigeria’s civil war and his steadfast commitment to justice, even enduring imprisonment for standing by his principles.
The president noted that Obasanjo continues to contribute to national development through advisory roles, writings, and engagement in major national issues.
Tinubu prayed for Obasanjo’s continued health, strength, and wisdom to enable him to keep serving Nigeria and humanity.
Tags
Labarai
