Shugaban Hezbollah ya sha alwashin ci gaba da yaƙi da Isra’ila.

Shugaban Hezbollah ya sha alwashin ci gaba da yaƙi da Isra’ila.

Shugaban ƙungiyar Hezbollah, Naim Qassem, ya sha alwashin cewa ƙungiyarsa za ta ci gaba da yaƙi da Israel duk da hare-haren bama-bamai da Isra’ila ke kaiwa a cikin Lebanon.

Qassem ya bayyana cewa ƙungiyar ba za ta daina gwagwarmaya ba muddin Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare tare da mamaye wasu yankuna a kudancin Lebanon.

Ya kuma yi watsi da shirin gwamnatin Lebanon na ƙwace makaman ƙungiyar Hezbollah. 
A cewarsa, makaman ƙungiyar na da muhimmanci wajen kare ƙasar daga hare-haren Isra’ila.

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da rikici tsakanin Hezbollah da Isra’ila ke ci gaba da ƙara tsananta, musamman a yankunan kudancin Lebanon.

News Translation in English Language.

Hezbollah Leader Vows to Continue Fight Against Israel.

Hezbollah leader Naim Qassem has pledged that the group will continue its fight against Israel, despite ongoing airstrikes and Israeli occupation of positions in southern Lebanon.

Qassem rejected the Lebanese government’s plans to disarm Hezbollah, saying the group’s weapons are crucial for defending the country against Israeli attacks.

His remarks come as tensions between Hezbollah and Israel continue to escalate, particularly in the southern regions of Lebanon.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form