Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa dakarunta sun kashe wani fitaccen mai garkuwa da mutane tare da ceto mutum huɗu da aka yi garkuwa da su a Jihar Edo.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana cewa dakarun rundunar ta 4 na sojin Najeriya sun kai samame a wani sansanin ‘yan bindiga da ke cikin daji a yankin Auchi da ke ƙaramar hukumar Etsako ta yamma, bayan samun sahihan bayanan sirri.
Rahotanni sun nuna cewa dakarun sun yi artabu da ‘yan bindigar, inda suka kashe wani shahararren mai garkuwa da mutane da ya dade yana addabar al’ummar yankin. Sauran ‘yan bindigar kuwa sun tsere zuwa cikin daji sakamakon matsin lambar da sojojin suka yi musu.
A yayin samamen, sojojin sun samu nasarar ceto mutane huɗu da aka yi garkuwa da su, waɗanda suka haɗa da Stella Abbas mai shekaru 29 da Tina Ododa mai shekaru 19 da Razak Rashid mai shekaru 27 da kuma Mutanibi Kalifa mai shekaru 16.
Dukkaninsu an tabbatar da cewa suna cikin koshin lafiya kafin a miƙa su ga iyalansu.
Hakazalika, sojojin sun kwato wasu kayayyaki daga hannun ɗan bindigar da aka kashe, ciki har da kuɗi kimanin naira 650,000, wayoyin hannu, da kuma wasu kayayyaki na sirri.
A wani samame na daban da aka kai a ƙauyen Ujemen da ke ƙaramar hukumar Esan ta yamma, dakarun sun kama wani da ake zargi da hannu a harkar garkuwa da mutane mai suna Omogbegha Solomon mai shekaru 39.
Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike kan wanda ake zargin, yayin da aka miƙa shi ga hukumomin tsaro domin ci gaba da gudanar da bincike da kuma ɗaukar matakin doka.
A cewar kwamandan rundunar ta 4, Ahmed Balogun, rundunar sojin za ta ci gaba da ƙarfafa ayyukan tsaro a faɗin jihar domin kawo ƙarshen ayyukan masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka.
News Translation in English Language.
Soldiers Kill Notorious Kidnapper, Rescue Four Victims in Edo.
The Nigerian Army has announced that its troops killed a notorious kidnapper and rescued four individuals who had been abducted in Edo State.
According to a statement from the army, soldiers from the 4 Brigade carried out an operation in a criminal hideout in the forest near Auchi, located in Etsako West Local Government Area, following verified intelligence reports.
During the raid, the troops engaged with the kidnappers, killing a prominent criminal who had long terrorized the local communities, while the remaining gang members fled into the forest.
The operation led to the safe rescue of four victims: Stella Abbas (29), Tina Ododa (19), Razak Rashid (27), and Mutanibi Kalifa (16). All were reported to be in good health and were returned to their families.
The army also recovered several items from the slain kidnapper, including approximately ₦650,000, mobile phones, and other personal belongings.
In a separate operation in Ujemen, Esan West Local Government Area, the troops arrested a suspected kidnapper, Omogbegha Solomon (39). The hideout contained ritualistic items and photographs, which were destroyed immediately, and the suspect was handed over to the police for further investigation.
Brigadier-General Ahmed Balogun, commander of 4 Brigade, praised the troops and vowed to continue operations to protect lives and property in Edo State, reinforcing efforts to curb kidnapping and criminal activities in the region.
Tags
Labarai
_2.jpg)