Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa matsalar rashin isasshen wutar lantarki da ake fama da ita a kwanakin nan za ta inganta nan ba da jimawa ba.
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wanda aka gudanar a Abuja a ranar Juma’a, 27 ga Maris.
Ya ce: “Ina tabbatar muku, da yawa daga cikinku na kokawa kan matsalar lantarki; muna mai da hankali sosai a kai. Wutar lantarki za ta inganta, kuma muna tabbatar muku za a samu dama da ci gaba a fannin masana’antu. Ta hanyar kamfanin kula da kadarorin wutar lantarki na Grid Asset Management Company, za mu ƙara kimanin megawatt 1,500 a wani sabon layin rarraba wutar lantarki.”
Tinubu ya ƙara da cewa tasirin shirye-shiryen gwamnatinsa a bayyane yake kuma ana iya aunawa, ba wai kalamai kawai ba kamar yadda wasu ‘yan adawa ke ikirari.
Ya ce: “Muna motsawa daga yanayin tsira kawai zuwa samun daidaito da kwanciyar hankali a tattalin arziki.”

0 Comments:
Post a Comment