Sakin El-Rufai cikin gaggawa ya nuna cewa bai aikata laifi ba — Masu Sharhi.


Wasu masu sharhi kan harkokin siyasa a Najeriya sun bayyana cewa sakin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, cikin gaggawa daga tsarewar da hukumar ICPC ke mashi yana nuni da cewa babu hujjar laifi a kansa.

A cewarsu, yadda aka tsare shi na wani lokaci ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ba, sannan daga bisani aka sake shi cikin gaggawa bayan labarin rasuwar Mahaifiyarsa, na ƙara nuna cewa zarge-zargen da ake yi masa ba su da ƙarfi ko kuma ba a kammala bincike yadda ya kamata ba.

Masu sharhin sun ƙara da cewa irin wannan lamari na iya janyo tambayoyi kan yadda hukumomi ke tafiyar da bincike, musamman ma idan abin ya shafi manyan ‘yan siyasa. 
Sun kuma yi gargadin cewa amfani da tsarewar ba tare da shari’a ba na iya zama wata hanya ta matsin lamba ga masu ra’ayi daban.

Sai dai a gefe guda, wasu masana harkokin shari’a sun jaddada cewa sakin mutum daga tsarewa ba yana nufin an wanke shi daga duk wani zargi ba. 
Sun bayyana cewa hukumomi na iya ci gaba da bincike, kuma za a iya sake gurfanar da shi idan an samu sabbin hujjoji.

Lamarin ya haifar da muhawara a tsakanin jama’a, inda wasu ke ganin an yi masa rashin adalci, yayin da wasu ke kira ga hukumomi da su tabbatar da bin doka da oda a dukkan matakai na bincike da shari’a.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: