Akalla sojojin Amurka uku ne suka mutu, yayin da wasu biyar suka jikkata sosai, sakamakon hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kai kan sansanonin sojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya, a cewar Rundunar sojin Amurka dake yankin Gabas ta tsakiya.
Rahoton ya ce mutuwar sojojin ta faru ne yayin da ake ci gaba da yaƙi da Amurka ke jagoranta kan Iran, biyo bayan hare-haren hadin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kai kan wasu muhimman wurare a Iran. Wannan shi ne karo na farko da Amurka ta tabbatar da asarar rayukan sojojinta tun bayan barkewar sabon rikicin.
Rundunar sojin Amurkan ta bayyana cewa sunayen sojojin da suka mutu ba za a bayyana ba har sai an sanar da iyalansu.
Haka kuma, an ce wasu sojoji sun samu raunuka masu sauki sakamakon fashewar makamai da girgizar bam.
A martaninta, Iran ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki (drones) kan wuraren da sojojin Amurka da kawayenta ke amfani da su a yankin, lamarin da ya kara tsananta rikicin.
Masana tsaro sun ce halin da ake ciki na iya kara tabarbarewa, yayin da kasashe da dama ke kira da a dakatar da fadace-fadacen tare da komawa teburin tattaunawa don kauce wa fadada rikicin a yankin.
News Translation in English Language.
Three U.S. Troops Killed in Iran Conflict — CENTCOM.
At least three U.S. service members have been killed, while five others were seriously wounded, following retaliatory attacks targeting U.S. military bases in the Middle East, according to U.S. Central Command (CENTCOM).
The statement said the deaths occurred as U.S.-led military operations against Iran continue, following **joint strikes by the United States and Israel on key locations inside Iran. This marks the first confirmed U.S. military fatalities since the latest phase of the conflict began.
CENTCOM noted that the identities of the fallen troops have not yet been released pending notification of their families. Several other personnel sustained minor injuries caused by explosions and blast shockwaves.
In response, Iran launched missile and drone attacks against facilities used by U.S. forces and their allies across the region, further escalating tensions.
Security analysts warn that the situation could deteriorate rapidly, as multiple countries urge an immediate halt to hostilities and a return to diplomatic talks to prevent the conflict from spreading further across the Middle East.
Tags
Labarai
_6.jpeg)