Aƙalla mutane huɗu ne suka rasa rayukansu bayan babban tudun shara ya rushe a wani wurin zubar da shara a ƙasar Indonesia, lamarin da ya janyo bacewar wasu mutanen da dama.
Lamarin ya faru ne a wurin zubar da shara na Bantargebang Landfill, wanda ke wajen birnin Jakarta. Rahotanni sun ce rushewar ta faru ne da rana bayan ruwan sama mai yawa ya sa tudun shara ya zama mai laushi kafin ya ruguje.
Jami’an ceto sun ce rushewar ta rufe wasu manyan motocin ɗaukar shara da kuma wasu rumfunan ’yan kasuwa da ke kusa da wurin. Wasu daga cikin waɗanda suka mutu sun haɗa da direbobin motocin shara da kuma ma’aikatan da ke tattara kayayyakin sake sarrafa sharan.
Hukumomi sun bayyana cewa aƙalla mutane biyar har yanzu ana zargin sun maƙale a ƙarƙashin sharan, yayin da sama da jami’an ceto 200, ciki har da ’yan sanda da sojoji, ke ci gaba da aikin neman waɗanda suka ɓace.
An kuma tura injunan tona ƙasa da karnukan gano mutane domin taimaka wa aikin ceto a wurin.
Wurin zubar da shara na Bantargebang yana daga cikin manyan wuraren zubar da shara a Indonesia, inda ake kai dubban ton na shara daga Jakarta da kewaye a kowace rana.
Hukumomi sun ce ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin aukuwar lamarin tare da ɗaukar matakan hana sake faruwarsa.
News Translation in English Language.
Landfill Collapse in Indonesia Kills Four, Several Missing.
At least four people have been confirmed dead after a massive pile of garbage collapsed at a landfill in Indonesia, authorities said.
The incident occurred at the Bantargebang Landfill located on the outskirts of Jakarta. Reports said the collapse happened in the afternoon following heavy rainfall that weakened the huge mound of waste before it gave way.
Rescue officials said the avalanche of garbage buried several dump trucks and small food stalls operating near the site. Some of the victims were believed to be truck drivers and waste pickers who were collecting recyclable materials at the landfill.
Authorities added that at least five people are still feared trapped under the debris. More than 200 rescue workers, including police and military personnel, have been deployed to the area to search for survivors.
Excavators and trained search dogs have also been brought in to assist in the rescue operation.
The Bantargebang landfill is one of the largest waste disposal sites in Indonesia, receiving thousands of tonnes of garbage daily from Jakarta and surrounding areas. Officials say investigations are ongoing to determine the cause of the collapse and prevent similar incidents in the future.
Tags
Labarai
