Iran ta harba makamai masu linzami zuwa Isra’ila da wasu ƙasashen yankin Gulf a safiyar Litinin, bayan da Jamhuriyar Musulunci ta ayyana Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran ƙasar domin maye gurbin mahaifinsa marigayi, duk da barazanar da Amurka da Isra’ila suka yi na cewa za su iya kai masa hari nan gaba.
Kwana tara bayan hare-haren haɗin gwiwa na Amurka da Isra’ila suka kashe Ayatollah Ali Khamenei tare da jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin wani sabon rikicin yaƙi, malaman addinin Iran sun zaɓi sabon jagora na uku tun bayan juyin juya halin Musulunci na shekarar 1979.
A lokaci guda kuma, Isra’ila ta ƙaddamar da sabon jerin hare-hare ta sama, inda a wannan karon ta kai hari kan muhimman gine-ginen more rayuwa a tsakiyar Iran.
Faɗaɗar yaƙin na ƙara jefa kasuwannin duniya cikin tashin hankali, inda kasuwannin hannayen jari suka yi ƙasa, yayin da farashin ɗanyen mai ya tashi da kusan kashi 30 cikin ɗari sakamakon fargabar tangardar samar da mai a kasuwannin duniya.
News Translation in English Language.
Iran Launches Missiles Toward Israel and Gulf States.
Iran fired missiles toward Israel and several Gulf States early Monday after the Islamic Republic named Mojtaba Khamenei as its new supreme leader to succeed his late father, despite threats from the United States and Israel that he could be targeted in future strikes.
Nine days after joint strikes by the United States and Israel killed Ayatollah Ali Khamenei and pushed the Middle East into a new phase of war, Iranian clerics selected the country’s third supreme leader since the Iranian Revolution.
At the same time, Israel launched a new wave of airstrikes, this time targeting key infrastructure in central Iran.
The widening conflict has shaken global markets, with stock markets falling while crude oil prices surged by nearly 30 percent, driven by fears of disruptions to global oil supply.
Tags
Labarai
