Mutane Aƙalla 42 ne Suka Rasa Rayukansu Sakon Ambaliyar Ruwa a Kenya.


Aƙalla mutane 42 ne suka mutu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a sassa daban-daban na ƙasar Kenya, bayan kwanaki ana samun ruwan sama mai ƙarfi.

Rahotanni sun nuna cewa mutane 26 daga cikin waɗanda suka mutu sun kasance a babban birnin ƙasar, Nairobi, inda ruwa ya mamaye gidaje, ya kwashe motoci, tare da haddasa nutsewa da wasu haɗurra.

Ambaliyar ta lalata hanyoyi da gidaje da ababen more rayuwa, yayin da ta kawo cikas ga zirga-zirgar jiragen sama a Filin Jirgin Sama na Jomo Kenyatta da kuma janyo cunkoson ababen hawa a manyan tituna.

Gwamnatin Kenya ta tura jami’an ceto da sojoji domin taimaka wa waɗanda abin ya shafa, yayin da shugaban ƙasa William Ruto ya ba da umarnin raba tallafin abinci daga ajiyar gwamnati ga iyalan da ambaliyar ta shafa.

Masana sun ce irin waɗannan ruwan sama masu karfi suna ƙaruwa a yankin Gabashin Afirka, kuma ana danganta hakan da sauyin yanayi (climate change) wanda ke ƙara tsananta haɗurran ambaliya.

News Translation in English Language.

At Least 42 Killed in Floods Across Kenya.

Nairobi, Kenya – At least 42 people have died following severe flooding across various parts of Kenya after days of heavy rainfall.

Officials reported that 26 of the fatalities occurred in the capital, Nairobi, where rising waters inundated homes, swept away vehicles, and caused drowning and other accidents.

The floods have damaged roads, homes, and infrastructure, while also disrupting air travel at Jomo Kenyatta International Airport and causing traffic congestion on major highways.

The Kenyan government has deployed rescue teams and military personnel to assist affected communities, and President William Ruto has ordered the distribution of food aid from government reserves to families impacted by the floods.

Experts say such extreme rainfall events are increasing in East Africa, attributing the trend to climate change, which is intensifying the risk of flooding.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form