Matan sojojin da ake zargi da shirin juyin mulki sun yi zanga-zanga kan tsaremazajensu tsawon kwanaki 160.

Matan sojojin da ake zargi da shirin juyin mulki sun yi zanga-zanga kan tsaremazajensu tsawon kwanaki 160.

Matan wasu jami’an sojin Najeriya da ake tsare da su bisa zargin yunkurin juyin mulki sun gudanar da zanga-zanga a Abuja, inda suka bukaci a gurfanar da mazajensu a kotu ko kuma a sake su. 

Matan sun bayyana cewa an tsare mazajensu sama da kwanaki 160 ba tare da an kai su gaban kotu ba, lamarin da suka ce ya saba wa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya. 

Zanga-zangar ta samu goyon bayan wasu masu fafutukar kare hakkin bil’adama da suka hada da Omoyele Sowore da lauya Deji Adeyanju, wadanda suka bukaci a gudanar da shari’a cikin gaskiya da adalci. 

Matan sun ce tun bayan kama mazajensu bisa zargin shirin kifar da gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ba su samu damar ganawa da su ba, kuma iyalansu na cikin fargaba da rashin tabbas. 

A cewarsu, sun fito ne domin neman a bi tsarin doka, inda suka jaddada cewa duk wanda ake zargi bai zama mai laifi ba har sai kotu ta tabbatar. Don haka suka bukaci gwamnati da rundunar sojin Najeriya su:

Ba su damar ganin mazajensu da ake tsare da su

Su gurfanar da su a kotu idan akwai hujja

Ko kuma su sake su idan babu hujjar da ta tabbatar da zargin

Matan sun kuma yi kira ga shugaban kasa da sauran masu ruwa da tsaki da su shiga tsakani domin tabbatar da cewa an gudanar da shari’ar cikin gaskiya da adalci. 

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form