Jiragen Yaƙin Iran Masu Linzami Da Marasa Matuƙa Sun Mamaye Sararin Samaniyar Isra’ila — Kakakin Sojin Iran.

Jiragen Yaƙin Iran Masu Linzami Da Marasa Matuƙa Sun Mamaye Sararin Samaniyar Isra’ila — Kakakin Sojin Iran..

Rundunar sojin ƙasar Iran ta bayyana cewa makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa da ƙasar ta harba sun fara mamaye sararin samaniyar yankunan da Israel ke iko da su.

A cewar wani kakakin rundunar sojin Iran, hare-haren da ƙasar ta kaddamar na ci gaba da ƙara ƙarfi, inda ya ce jiragen yaƙin marasa matuƙa da makamai masu linzami na Iran suna shiga sararin samaniyar Isra’ila cikin sauƙi duk da ƙoƙarin tsarin kariyar iska na Isra’ila.

Rahotanni sun nuna cewa an ji karar fashe-fashe a sassa daban-daban na Isra’ila, ciki har da birnin Tel Aviv, yayin da makamai masu linzami da aka harba suka rika shiga sararin samaniyar ƙasar, wasu kuma tsarin kariyar iska ya rika tarwatsa su.

Wannan sabon ikirari na Iran ya zo ne a daidai lokacin da rikicin yaƙi ke ƙara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya, bayan jerin hare-haren ramuwar gayya tsakanin Iran da Isra’ila, lamarin da ya jawo tashin hankali a yankin.

Iran ta ce hare-haren nata wani ɓangare ne na martanin da take mayarwa kan hare-haren da ta zargi Isra’ila da ƙawayenta da kai wa wasu wurare a cikin ƙasar.

Sai dai hukumomin Isra’ila ba su yi cikakken bayani ba game da ikirarin na Iran, amma sun ce tsarin kariyar iska na ƙasar na ci gaba da aiki domin dakile duk wata barazana daga makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa.

Masu lura da al’amuran tsaro na duniya na gargadin cewa wannan sabon yanayi na iya ƙara jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin wani babban rikici idan ba a samu matakan sassauta rikicin ba.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form