Rundunar kare juyin juya halin ƙasar Iran, wato IRGC, ta sanar da kaddamar da wani sabon zagaye na hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan Isra’ila da wasu wuraren soji da ke da alaƙa da Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce harin na daga cikin wani gagarumin farmaki da ake kira “True Promise 4”, wanda aka ce an yi amfani da sabbin ƙarni na makamai masu linzami masu saurin kai hari da kuma jirage marasa matuƙa domin kai farmaki kan muhimman wuraren soji.
IRGC ta ce hare-haren sun shafi wasu wuraren da ake zargin sojojin Amurka ke amfani da su a ƙasashen Bahrain da Kuwait da Jordan baya ga wuraren soji na Israel.
Rundunar ta bayyana cewa wannan mataki na daga cikin martanin Iran kan hare-haren da United States da Isra’ila suka kai a wasu wurare a cikin Iran a kwanakin baya, wanda ya kara tsananta rikicin da ake fama da shi a yankin.
Rahotanni sun ce wasu makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa sun ratsa sararin samaniyar wasu ƙasashen yankin, lamarin da ya sa hukumomi suka ɗauki matakan gaggawa na tsaro domin kare manyan cibiyoyi da sansanonin soji.
Masu nazarin harkokin tsaro na gargadi cewa rikicin na iya ƙara tsananta, inda ake fargabar cewa zai iya rikidewa zuwa babban rikicin soja a yankin Gabas ta Tsakiya idan ba a samu sassauci ba.
News Translation in English Language.
IRGC Launches New Missile Strikes on Israel and US-Linked Bases in the Middle East.
Tehran – Iran’s Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) has announced a new wave of missile and drone attacks targeting Israel and military sites linked to the United States in the Middle East.
The operation, dubbed “True Promise 4,” reportedly involved the use of next-generation missiles and unmanned aerial vehicles to strike strategic military locations.
According to the IRGC, the strikes hit sites in Bahrain, Kuwait, and Jordan, as well as military installations in Israel.
The Iranian military described the attacks as a retaliatory response to recent strikes carried out by the US and Israel inside Iran, escalating tensions across the region.
Reports indicate that some missiles and drones crossed the airspace of neighboring countries, prompting authorities to implement emergency security measures to protect critical infrastructure and military bases.
Analysts warn that the conflict could further intensify, with the risk of a broader military confrontation in the Middle East if tensions continue to escalate.
Tags
Labarai
