Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Bindiga 45 a Katsina, ya yin da suka rasa Kyaftin da Sojoji Biyu.

Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Bindiga 45 a Katsina, ya yin da suka rasa Kyaftin da Sojoji Biyu.

Dakarun rundunar sojin Najeriya sun kashe akalla ‘yan bindiga 45 a wani mummunan artabu da suka yi da su a jihar Katsina, yayin da rundunar ta yi rashin kyaftin ɗaya da sojoji biyu a yayin fafatawar.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a wasu yankunan ƙaramar hukumar Danmusa bayan jami’an tsaro sun samu bayanan sirri kan motsin ‘yan bindigar da ke shirin kai hari.

A cewar jami’an tsaro na jihar, ‘yan bindigar sun shigo yankin ne daga jihar Zamfara dauke da makamai a kan babura domin kai hari ga al’umma tare da sace shanu a kauyen Alhazawa da ke ƙaramar hukumar Musawa.

Sai dai mazauna yankin tare da wasu tsofaffin ‘yan bindiga da suka tuba sun yi musu turjiya, inda suka kashe ‘yan bindiga huɗu tare da kwato shanun da aka sace.

Rahoton ya kara da cewa washegari ‘yan bindigar sun sake dawowa da yawa domin daukar fansa, amma suka ci karo da dakarun sojoji da ke sansanin Forward Operating Base a Dan Ali, wanda ya haddasa mummunar musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.

A sakamakon artabun, sojojin sun kashe ‘yan bindiga 45, ciki har da wasu fitattun jagororinsu, yayin da sauran suka tsere da raunuka.

Sai dai rundunar sojin ta yi rashin Kyaftin Paul Hassan da wasu sojoji biyu da suka rasu yayin da suke fafatawa da ‘yan bindigar.

Gwamnatin jihar Katsina ta yaba da jarumtakar sojojin tare da jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu, tana mai cewa sadaukarwar da suka yi ta taimaka wajen kare rayukan al’umma da kuma dakile ayyukan ‘yan bindiga a yankin.

News Translation in English Language.

Military Kills 45 Bandits in Katsina, Loses Captain and Two Soldiers.

The Nigerian military has killed at least 45 bandits in a major clash in Katsina State, while suffering the loss of one captain and two soldiers during the operation.

Reports indicate that the confrontation occurred in parts of Danmusa Local Government Area after security forces received credible intelligence about the movements of bandits planning attacks.

According to state security officials, the bandits came from Zamfara State armed with weapons and motorcycles, intending to raid communities and steal cattle in Alhazawa village, Musawa LGA.

Local residents, along with some repentant former bandits, resisted the attackers, killing four bandits and recovering the stolen cattle.

The following day, the bandits returned in larger numbers seeking revenge but clashed with military forces stationed at the Forward Operating Base in Dan Ali, resulting in heavy gunfire exchange.

The operation resulted in the death of 45 bandits, including some of their top leaders, while others fled with injuries.

However, the military lost Captain Paul Hassan and two soldiers in the fighting.

The Katsina State government praised the bravery of the military, extended condolences to the families of the fallen soldiers, and stated that their sacrifice helped protect lives and curb banditry in the region.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form