Makamai masu linzami da Iran ta harba sun haifar da fashe-fashe a tsakiyar birnin Tel Aviv na Israi'la.

Makamai masu linzami da Iran ta harba sun haifar da fashe-fashe a tsakiyar birnin Tel Aviv na Israi'la.

An ji ƙarar fashe-fashe a tsakiyar birnin Tel Aviv bayan da ƙasar Iran ta harba jerin makamai masu linzami zuwa cikin Israel, a daidai lokacin da rikicin ke Ƙara tsananta a tsakanin Ƙasashen.

Rahotanni sun bayyana cewa tsarin kariyar sama na Isra’ila ya yi ƙoƙarin tare wasu daga cikin makaman da aka harba, amma duk da haka an ji fashe-fashe a wasu sassan birnin, lamarin da ya sa aka kunna ƙararrawar gaggawa tare da umartar mazauna yankin su shiga mafaka domin tsira.

Shaidu sun ce an ga hayaƙi yana tashi daga wasu wurare bayan harin, yayin da jami’an agajin gaggawa da na kashe gobara suka garzaya wurin domin duba irin ɓarnar da aka yi da kuma taimaka wa waɗanda abin ya shafa.

Hukumomin Isra’ila sun ce ana ci gaba da tattara bayanai kan harin, tare da binciken ko an samu asarar rayuka ko raunuka, yayin da aka kuma samu lalacewar wasu gine-gine sakamakon fashe-fashe.

Harin dai na zuwa ne a wani lokaci da rikici ke ƙara ƙamari tsakanin Iran da Israi'la da Amurka, inda bangarorin ke ci gaba da zargin juna da kai hare-hare, abin da ke ƙara tayar da hankalin ƙasashen duniya kan yiwuwar faɗaɗar yaƙi a yankin.

News Translation in English Language.

Iran Missile Barrage Triggers Explosions Over Tel Aviv

Explosions were heard across Tel Aviv after Iran launched a barrage of missiles toward Israel, escalating tensions in the Middle East.

Reports indicate that Israel’s air defence systems attempted to intercept several of the incoming missiles. However, blasts were still heard in parts of the city, prompting emergency sirens and forcing residents to rush into shelters for safety.

Eyewitnesses reported seeing smoke rising from some areas following the attack, as emergency responders and firefighters moved quickly to the affected locations to assess the damage and assist those impacted.

Israeli authorities said investigations were ongoing to determine the extent of the damage and whether there were casualties or injuries. Initial reports suggest that some buildings were damaged by the explosions.

The attack comes amid growing tensions between Iran and Israel, with both sides trading accusations over recent military actions, raising fears of a wider conflict in the region.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form