Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa Amurka a halin yanzu ba ta tunanin tura sojojin ƙasa zuwa Iran, duk da ci gaba da tashin hankalin da ake samu a yankin gabas ta tsakiya.
Trump ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da kafar yaɗa labarai ta NBC News, inda ya ce matakin tura sojojin ƙasa zai zama abu mai wahala kuma ba shi ne abin da Amurka ke la’akari da shi a yanzu ba.
Sai dai Trump ya jaddada cewa Amurka na ci gaba da sanya ido kan halin da ake ciki, musamman rikicin da ke ƙara tsananta tsakanin Israi'la da Iran, wanda ya jawo hare-haren makamai da dama a yankin.
Ya kuma yi ikirarin cewa Iran ta riga ta yi asara mai yawa a rikicin da ke gudana, yana mai cewa wasu daga cikin muhimman kayan yaƙinta sun lalace sakamakon hare-haren da ake kai mata.
Duk da haka, Trump ya ce Amurka za ta ci gaba da ɗaukar matakan kare muradunta da kuma na ƙawayenta a yankin, amma ya jaddada cewa ba a cikin shirin gwamnatin Amurka a yanzu ba ne tura sojojin ƙasa zuwa Iran.
Furucin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin da ke tsakanin Iran da Isra’ila ke ƙara tsananta, lamarin da ya janyo fargaba game da yiwuwar faɗaɗa yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya.
News Translation in English Language.
Trump Says US Not Considering Deployment of Ground Troops to Iran.
Former US President Donald Trump has said that the United States is not considering deploying ground troops to Iran, despite rising tensions in the Middle East.
Trump made the remark during an interview with NBC News, noting that sending ground forces would be a difficult move and is not currently under consideration by the US.
However, he stressed that the United States is closely monitoring developments in the region, particularly the escalating conflict involving Israel and Iran, which has triggered several missile and military exchanges.
Trump also claimed that Iran has already suffered significant losses in the ongoing confrontation, stating that some of its key military assets have been damaged during the attacks.
He added that the United States would continue to protect its national interests and those of its allies in the region, but emphasized that deploying ground troops to Iran is not part of the current plan.
His comments come amid growing tensions between Iran and Israel, raising fears that the conflict could expand further across the Middle East.
Tags
Labarai
