Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta wanke tsohon Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda, Abba Kyari, daga zargin kin bayyana kadarorinsa.
Alkalin kotun, James Omotosho, ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis bayan ya bayyana cewa masu gabatar da ƙara sun gaza gabatar da hujjoji masu ƙarfi da za su tabbatar da zargin da ake yi wa Kyari.
Hukumar Hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ce ta gurfanar da Kyari tare da ‘yan uwansa biyu — Mohammed Kyari da Ali Kyari — a gaban kotu kan tuhume-tuhume guda 23 da suka shafi kin bayyana wasu kadarori da kuma zargin ɓoye mallakar wasu gidaje.
Sai dai alkalin kotun ya ce bangaren masu gabatar da ƙara sun kasa tabbatar da cewa kadarorin da ake magana a kai mallakin Kyari ne, domin ba su gabatar da sahihan takardun mallaka ko wasu hujjojin da za su tabbatar da hakan ba.
Kotun ta kuma lura cewa wasu daga cikin kadarorin da aka ambata an bayyana cewa na mahaifin Kyari ne da ya rasu, kuma masu gabatar da ƙara ba su iya tabbatar da akasin hakan ba.
Sai dai duk da wannan hukunci, ana ci gaba da shari’ar da ake yi wa Kyari a wata daban da ta shafi zargin safarar miyagun ƙwayoyi tare da wasu jami’an ‘yan sanda.
Tags
Labarai
