Majalisar Kwararrun Iran Ta Cimma Matsaya Kan Wanda Zai Gaji Khamenei

Majalisar Kwararrun Iran Ta Cimma Matsaya Kan Wanda Zai Gaji Khamenei

Majalisar malamai ta Iran mai suna majalisar kwararru ta bayyana cewa ta cimma cikakkiyar matsaya kan wanda zai gaji jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei.

Rahotanni sun nuna cewa mafi yawan mambobin majalisar sun riga sun amince da mutumin da zai zama sabon jagoran addini na ƙasar, sai dai har yanzu ana kammala wasu matakan shari’a da tsarin doka kafin a sanar da sunansa a hukumance.

Wani mamba a majalisar, Ayatollah Mohammad‑Mahdi Mirbagheri, ya bayyana cewa an samu yarjejeniya tsakanin mafi yawan malamai kan wanda zai gaji jagorancin ƙasar, amma ana ci gaba da tattaunawa kan yadda za a tabbatar da zaɓen bisa tsarin doka.

A cewarsa, halin da ƙasar ke ciki na rikice-rikicen tsaro da barazanar hare-hare ya sanya ya zama da wuya a gudanar da cikakken taron majalisar a wuri guda domin kammala sanarwar.

Rahotannin cikin gida sun kuma ce zaɓen wanda zai zama sabon jagoran ya yi daidai da shawarar da marigayi Khamenei ya taɓa bayarwa cewa jagoran Iran ya kasance mutum mai tsayin daka wanda ba zai bi ra’ayin ƙasashen waje ba.

Har yanzu ba a bayyana sunan wanda aka zaɓa ba, amma wasu rahotanni na hasashen cewa Mojtaba Khamenei, ɗan marigayin jagoran, na cikin mutanen da ake ganin suna da damar maye gurbinsa.

Jagoran addini na Iran shi ne mafi girman mai iko a tsarin siyasar ƙasar, inda yake da ikon jagorantar manyan manufofin ƙasa tare da kula da rundunar soji da harkokin tsaro.

Ana sa ran majalisar za ta sanar da sunan sabon jagoran Iran a hukumance nan gaba kaɗan bayan kammala dukkan matakan da suka dace.

News Translation in English Language.

Iran’s Assembly of Experts Near Consensus on Khamenei’s Successor.

Iran’s clerical body, the Assembly of Experts, has reportedly reached near consensus on who will succeed Ayatollah Ali Khamenei as the country’s Supreme Leader.

Reports indicate that most members of the assembly have agreed on a candidate, though some legal and procedural matters still need to be finalized before an official announcement can be made.

Ayatollah Mohammad-Mahdi Mirbagheri, a member of the assembly, said that while broad agreement has been achieved, discussions are ongoing to ensure the selection process aligns with legal and procedural requirements.

Security concerns and threats of attacks have complicated the process, making it difficult to hold a full assembly session in one location to finalize the decision.

Domestic reports indicate that the selection aligns with guidance previously given by Khamenei, emphasizing a successor who will remain firm and independent of foreign influence.

Although no official name has been announced, some reports suggest that Mojtaba Khamenei, the son of the late Supreme Leader, is among the leading candidates.

The Supreme Leader holds the highest authority in Iran’s political system, overseeing military, security, and major national policy decisions.

The assembly is expected to formally announce the new Supreme Leader once all procedural steps are completed.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form