Israi'lawa 'yan kama wuri zauna sun Kashe Falasɗinawa mutum uku a yammacin Kogin Jordan.

Israi'lawa 'yan kama wuri zauna sun Kashe Falasɗinawa mutum uku a yammacin Kogin Jordan.

Jami’an Falasɗinu sun bayyana cewa wasu Israi'lawa ‘yan kama wuri zauna sun kashe mutane uku Falasɗinawa a hare-haren da suka faru a yankin Yammacin Kogin Jordan.

Wani jami’in Falasɗinu ya ce lamarin ya faru ne a wasu rikice-rikice da suka barke tsakanin Falasɗinawa da ‘yan kama wuri zauna a yankin, inda aka yi ta harbe-harbe da jifan juna da duwatsu.

Rahotanni sun ce daga cikin wadanda aka kashe akwai ’yan’uwa biyu Falasɗinawa da aka harbe a wani kauye da ke yankin. 
Mutanen yankin sun zargi ‘yan kama wuri zauna da bude musu wuta yayin da rikici ya kaure.

Bayan haka kuma, wani Falasɗine na uku ya mutu sakamakon harbin bindiga a wani rikici da ya faru a kudancin yankin yammacin kogin Jordan.

Jami’an lafiya na Falasɗinu sun tabbatar da mutuwar mutanen uku tare da jikkatar wasu da dama da aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa.

A nata bangaren, rundunar sojin Israel ta ce tana binciken lamarin domin gano hakikanin abin da ya faru, yayin da ake zargin cewa daya daga cikin masu harbin bindigar wani sojan ajiyar Isra’ila ne.

Rikice-rikicen da ke tsakanin Falasɗinawa da Israi'lawa ‘yan kama wuri zauna a yankin yammacin kogin Jordan na kara kamari a ‘yan shekarun nan, lamarin da kungiyoyin kare hakkin bil’adama ke cewa yana haddasa asarar rayuka da kuma jikkata mutane da dama.

News Translation in English Language.

Israeli Settlers Kill Three Palestinians in West Bank.

Palestinian officials have reported that Israeli settlers have killed three Palestinians in a series of incidents across the West Bank.

According to local sources, clashes erupted between Palestinians and the settlers, involving gunfire and stone-throwing. Among the victims were two Palestinian brothers shot in a village in the area, while a third Palestinian died in a separate shooting incident in the southern part of the West Bank.

Health authorities confirmed the deaths and reported that several others were injured and rushed to hospitals for treatment.

The Israel Defense Forces stated that they are investigating the incidents, amid reports suggesting that one of the shootings may have involved a reservist soldier.

Human rights organizations have warned that such attacks by settlers are on the rise in the West Bank, contributing to loss of life, injuries, and displacement of Palestinians from their homes.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form