Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya tabbatar da cewa Iran tana da cikakken haƙƙi na mayar da martani idan aka kai mata hari daga kowace ƙasa.
A cewarsa, “Idan maƙiyanmu suka kai hari ko shiga ƙasarmu daga kowace ƙasa, dole ne mu mayar da martani. Wannan ba yana nufin muna da matsala da ƙasar ko muna son haifar da fushi ga al’ummar ta.”
Pezeshkian ya bayyana Iran a matsayin abokiya kuma 'yar’uwa ga ƙasashen yankin, yana mai cewa ya zama dole su haɗa kai domin tarwatsa makircin Amurka da Isra’ila.
Ya kuma jaddada bukatar Iran da makwabtan ta su warware matsalolinsu a gida, duk da ƙoƙarin maƙiya na ja su cikin rikici da yaki.
“Za mu tsaya tsayin daka wajen kare ƙasarmu daga duk wanda ya kai hari. Sojojinmu da ƙungiyar Basij da ke ƙasar za su kare ƙasa da duk ƙarfin su,” in ji Pezeshkian.
Ya ƙara da cewa Iran ba za ta lamunce zalunci da danniya ko cin zarafi ba. Haka kuma, ya roki gafara ga al’ummar yankin da ke cikin damuwa sakamakon yanayin siyasa mai rikitarwa a yankin.
Tags
Labarai
