Isra’ila Ta Kai Hari Kan Manyan Tashoshin Mai Na Iran.

Isra’ila Ta Kai Hari Kan Manyan Tashoshin Mai Na Iran.

A yau, Isra’ila ta kai harin jiragen sama kan manyan tashoshin ajiyar mai da cibiyoyin canja wurin mai a yankin Tehran da Alborz, wanda shi ne karo na farko da irin wannan abu ya faru tun bayan barkewar yakin da ke tsakanin kasashen biyu.

Rahotanni daga hukumomin Iran sun ce harin ya haddasa wuta mai girma da hayaki mai yawa, inda aka samu mutuwar akalla mutane hudu, yayin da sauran mutane da dama suka ji rauni. An kuma bayyana cewa harin na iya haifar da matsalolin muhalli da lafiyar jama’a.

Wannan hari na zuwa ne cikin wani yanayi na tashin hankali tsakanin Isra’ila da Iran, wanda ya kunshi harin makamai da jiragen sama na Amurka da Isra’ila a kan Iran. 
Iran ta mayar da martani da harin makamai masu linzami da jiragen sama masu saukar ungulu kan wasu cibiyoyi a yankin Gulf, ciki har da Bahrain, inda wasu ma’aikatu suka lalace.

Masu sharhi na ganin cewa kai hari kan cibiyoyin makamashin mai wani mataki ne na kara tsananta rikicin, saboda irin wannan abu yana da matukar tasiri ga tattalin arziki da muhalli. Hukumomin lafiya sun gargadi mutane su rage fita a waje saboda hayakin da ke dauke da guba.

News Translation in English Language.

Israel Strikes Iran’s Major Oil Facilities in First Targeted Attack.

Tehran, Iran – Israel launched airstrikes today on key oil storage sites and transfer centers around Tehran and Alborz province, marking the first time such infrastructure has been targeted since the ongoing conflict escalated.

Iranian authorities reported that the strikes caused large fires and thick smoke, resulting in at least four deaths and several injuries. Officials also warned of potential environmental and health hazards due to the widespread smoke.

The attack comes amid a broader confrontation between Israel and Iran, which has included strikes by U.S. and Israeli forces. Iran has responded with missile and drone attacks on facilities in the Gulf region, including Bahrain, damaging infrastructure and causing injuries.

Analysts say that targeting energy infrastructure represents a significant escalation, as it has far-reaching consequences for both the economy and the environment. Health authorities have urged residents to stay indoors due to the toxic smoke.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form