Iran Ta Shirya Taron Kwana Uku Don Yin Bankwana Da Marigayi Ayatollah Ali Khamenei.

Iran Ta Shirya Taron Kwana Uku Don Yin Bankwana Da Marigayi Ayatollah Ali Khamenei.

Jamhuriyar Muslunci ta Iran ta sanar da shirya taron kwanaki uku na jana’iza da bankwana domin girmama marigayi Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatollah Ali Khamenei.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Iran, Press TV, ya ruwaito cewa taron zai fara ne daga daren Talata a Tehran, inda dubban ‘yan kasar za su halarta domin yin addu’a da nuna jimami ga jagoran da ya rasu.

A cewar rahoton, za a gudanar da taron bankwana ne a babban masallacin Grand Mosalla, daya daga cikin manyan wuraren taro na addini a birnin Tehran. 
Gwamnati ta gayyaci al’umma daga sassa daban-daban na kasar domin halartar taron, wanda ake sa ran zai ja hankalin jama’a masu yawa.

Hukumomin Iran sun bayyana cewa wannan shiri na kwanaki uku na nuni ne da girmamawa da matsayi na musamman da marigayi Ayatollah Khamenei yake da shi a zukatan al’ummar Iran da kuma duniyar Musulunci baki daya.

Rahoton ya kara da cewa za a sanar da cikakkun bayanai game da jana’iza da wurin binne marigayin bayan kammala taron bankwana a Tehran.

News Translation in English Language.

Iran Announces Three-Day Farewell Ceremony for Late Ayatollah Ali Khamenei.

The Islamic Republic of Iran has announced plans to hold a three-day public farewell ceremony in honour of the late Supreme Leader, Ayatollah Ali Khamenei.

According to Iranian state broadcaster Press TV, the ceremony will begin on Tuesday night in Tehran, where large crowds are expected to gather to pay their final respects and offer prayers for the late leader.

The farewell events will be held at the Grand Mosalla, one of Tehran’s largest religious venues, traditionally used for major national and religious gatherings. Authorities have invited members of the public from across the country to participate in the ceremonies.

Iranian officials said the three-day programme reflects the high stature and influence of Ayatollah Khamenei, who led the Islamic Republic for decades and played a central role in shaping Iran’s political and religious landscape.

Further details regarding the funeral procession and burial arrangements are expected to be announced after the conclusion of the farewell ceremonies in Tehran.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form