Sojojin Nijeriya Sun Tura ‘jami'an gandun daji’ 170 Don Kare Al’ummomin Kebbi Masu Fuskantar Barazana.

Sojojin Nijeriya Sun Tura ‘jami'an gandun daji’ 170 Don Kare Al’ummomin Kebbi Masu Fuskantar Barazana.

Rundunar Sojojin Nijeriya ta sanar da tura jami’an kula da gandun daji su 170 zuwa wasu yankuna masu rauni a Jihar Kebbi, domin ƙarfafa tsaro da kare al’umma daga ayyukan ‘yan ta’adda da ‘yan fashi.

An tura jami’an ne zuwa Ƙaramar Hukumar Arewa ta jihar, inda aka bayyana cewa za su yi aiki a karkashin kulawar rundunar soji domin sa ido da kuma yaƙi da masu aikata laifuka a dazuzzuka da yankunan da ke da wahalar isa.

Babban Hafsan Sojojin yankin, Manjo Janar Bemgba Paul Koughna, wanda shi ne GOC na Runduna ta 8 kuma Kwamandan Sashen 2 na Operation Fansan Yamma, ya ce wannan mataki na da nufin toshe hanyoyin da masu aikata laifi ke amfani da su wajen kai hare-hare da satar mutane.

A cewarsa, domin tallafa wa aikin, rundunar ta samar da babura guda 10, kayan kwana 170, da kuma abinci, don ƙara ƙarfin motsi, walwala da kuma saurin mayar da martani na jami’an da aka tura.

A nasa bangaren, gwamnatin jihar Kebbi ta yaba da wannan mataki, inda Kwamishinan Harkokin Cikin Gida da Tsaro na jihar, Haliru Aliyu Wasabu, ya ce haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da sojoji na da matuƙar muhimmanci wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin.

Masana harkokin tsaro na ganin cewa wannan tura jami’ai zai taimaka matuƙa wajen rage ayyukan ‘yan fashi da garkuwa da mutane a yankunan karkara da dazuzzukan jihar Kebbi, musamman a Arewa maso Yammacin Nijeriya.

News Translation in English Language.

Nigerian Army Deploys 170 Forest Guards to Protect Vulnerable Communities in Kebbi.

The Nigerian Army has deployed 170 forest guards to vulnerable areas of Kebbi State as part of renewed efforts to strengthen security and protect rural communities from criminal activities.

The forest guards have been deployed to Arewa Local Government Area, where they will operate under the supervision of the Army to enhance surveillance and combat banditry, kidnapping and other security threats, particularly in forested and hard-to-reach locations.

Speaking during the deployment, Major General Bemgba Paul Koughna, the General Officer Commanding 8 Division and Commander of Sector 2, Operation Fansan Yamma, said the move was aimed at denying criminal elements access to forests often used as hideouts for launching attacks on communities.

To support the operation, the Army provided 10 new motorcycles, 170 sleeping kits, and food supplies to improve the mobility, welfare and operational effectiveness of the deployed personnel.

The Kebbi State Government welcomed the initiative, with the Commissioner for Home Affairs and Internal Security, Haliru Aliyu Wasabu, commending the Army for its commitment to restoring peace. He stressed that sustained collaboration between the military and the state government remains critical to addressing insecurity in the area.

Security analysts say the deployment is expected to significantly reduce criminal activities in Kebbi’s rural communities and contribute to improved safety across Nigeria’s North-West region.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form