Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa wani mummunan hari da aka kai kan wani asibiti a ƙasar Sudan ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutane 64, ciki har da yara 13.
A cewar rahotanni, harin ya kuma jikkata mutane da dama, yayin da ake ci gaba da fama da rikici mai tsanani a ƙasar, wanda ke haddasa babbar asarar rayuka da dukiyoyi ga fararen hula.
Hukumar ta WHO ta nuna matuƙar damuwa kan yadda ake kai hare-hare kan cibiyoyin kiwon lafiya, tana mai jaddada cewa irin waɗannan ayyuka na barazana ga rayuwar marasa lafiya da ma’aikatan lafiya, tare da ƙara ta’azzara matsalar jin kai a Sudan.
Rikicin da ke ci gaba da gudana a Sudan ya janyo lalacewar muhimman ababen more rayuwa, musamman a bangaren lafiya, lamarin da ke sa samun kulawa ga marasa lafiya ya ƙara zama ƙalubale.
Hukumar ta WHO ta yi kira ga dukkan ɓangarorin da ke rikicin da su mutunta dokokin ƙasa da ƙasa, musamman waɗanda ke kare fararen hula da cibiyoyin lafiya.

0 Comments:
Post a Comment