Gwamnatin Jihar Jigawa ta sanar da ƙara alawus ɗin da ake bai wa shugabannin unguwanni (Mai-unguwa) daga Naira 3,000 zuwa Naira 10,000 a kowane wata domin ƙarfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukansu a matakin ƙasa.
Sanarwar ta fito ne bayan taron Majalisar Zartarwar Jihar da aka gudanar a birnin Dutse, inda gwamnatin ta bayyana cewa matakin zai taimaka wajen inganta rawar da shugabannin gargajiya ke takawa a cikin al’umma.
Gwamnan jihar, Umar Namadi, ya amince da karin alawus ɗin, wanda ya ƙaru da Naira 7,000 daga abin da ake biya a baya. Gwamnatin ta ce an ɗauki wannan mataki ne la’akari da muhimmiyar gudunmawar da shugabannin unguwanni ke bayarwa wajen kula da al’umma da kuma taimaka wa gwamnati wajen isar da manufofi ga jama’a.
Shugabannin unguwanni na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da sasanta rikice-rikice a tsakanin mazauna yankunansu, da kuma zama gada tsakanin gwamnati da al’umma a matakin ƙasa.
A wani bangare kuma, majalisar zartarwar ta amince da gabatar da kudirin dokar kafa Jami’ar Kimiyyar Lafiya da Harkokin Lafiya ta Jihar Jigawa ga Majalisar Dokokin Jihar domin ƙara faɗaɗa damar ilimi a fannin kiwon lafiya a jihar.
News Translation in English Language.
Jigawa Increases Ward Heads’ Allowance from ₦3,000 to ₦10,000.
The Jigawa State Government has approved an increase in the monthly allowance of ward heads, popularly known as Maiunguwa, from ₦3,000 to ₦10,000 as part of efforts to support grassroots traditional leadership.
The decision was reached during a State Executive Council meeting held in Dutse, where officials explained that the move was intended to strengthen the role of ward heads in community administration.
Governor Umar Namadi approved the increase, which represents a ₦7,000 rise from the previous allowance. According to the government, the adjustment reflects the importance of ward heads in maintaining order and assisting authorities at the grassroots level.
Ward heads play a key role in their communities by helping to maintain peace, resolving minor disputes among residents, and serving as a link between the government and local populations.
In a related development, the State Executive Council also approved the submission of a bill to the State House of Assembly for the establishment of the Jigawa State University of Medical and Allied Health Sciences, aimed at expanding medical education and healthcare training in the state.
Tags
Labarai
