Gwamnan Jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya karrama jarumin shirin talabijin na Labarina, Kabiru Abubakar wanda aka fi sani da KB Danyarbawa, ta hanyar ba shi kujerar zuwa aikin Hajji.
KB Danyarbawa ya fito a cikin shahararren shirin Labarina inda ya taka rawar Jami’in Bincike na KEFCC a zango na 14, rawar da ta kara masa farin jini a wajen masu kallo.
Rahotanni sun nuna cewa Kabiru Abubakar ma’aikaci ne a Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Neja. Haka kuma mawaki ne da ke amfani da wakoki da gajerun bidiyoyin talla (jingles) wajen tallata ayyukan Gwamna Bago tun lokacin da yake dan majalisar tarayya.
Da yake bayyana jin dadinsa, KB Danyarbawa ya ce wannan dama da gwamnan ya ba shi ta zuwa aikin Hajji babbar karramawa ce a gare shi, domin ibadar Hajji na daya daga cikin manyan ginshikan addinin Musulunci.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya saka wa gwamnan da alheri, tare da fatan Allah Ya ba shi ikon sauke wannan ibada cikin koshin lafiya idan lokacin ya yi.
— Ahmad Nagudu
Media Manager, Labarina Series.
News Translation in English Language.
Niger State Governor Rewards Labarina Actor with Hajj Seat.
The Governor of Niger State, Umaru Mohammed Bago, has honoured Labarina television series actor Kabiru Abubakar, popularly known as KB Danyarbawa, by granting him a seat to perform the Hajj pilgrimage.
KB Danyarbawa gained popularity for his role as a KEFCC Investigating Officer in season 14 of the widely watched Hausa TV series Labarina.
Reports indicate that Kabiru Abubakar is also a staff member of the Niger State Fire Service. In addition, he is a musician who has been promoting Governor Bago through songs and short promotional videos (jingles) since the governor’s days as a member of the House of Representatives.
Speaking after receiving the honour, KB Danyarbawa expressed deep appreciation to the governor, describing the opportunity to perform Hajj as a great privilege, noting that the pilgrimage is one of the five pillars of Islam.
He also prayed for Allah to reward the governor abundantly and grant him the opportunity to perform the pilgrimage successfully when the time comes.
— Ahmad Nagudu
Media Manager, Labarina Series
