Wata gobara ta tashi a sashen kula da marasa lafiya mai tsanani (ICU) a asibitin SCB Medical College a yankin Cuttack dake jihar Odisha, a gabashin Indiya a safiyar yau Litinin.
Hukumomin lafiya a yankin sun bayyana cewa mutane 10 ne suka rasu a lokacin da ma’aikatan asibitin ke ƙoƙarin kawar da marasa lafiyar zuwa wurare masu aminci daga gobarar.
An ce marasa lafiya 23 ne ke cikin wurin (ICU) a lokacin da gobarar ta tashi.
Bincike na farko ya nuna cewa matsalar wutan lantarki ce mafi yiwuwar sanadiyyar gobarar, lamarin da ake yawan fuskanta musanman a gine-ginen da ba a kula da wayoyi da na’urorin lantarki yadda ya kamata.
Hukumar asibitin ta tabbatar da cewa ma’aikata da jami’an tsaro sun ji rauni yayin da suke ceto marasa lafiya.
Firaministan Indiya, Narendra Modi, ya bayyana wannan al’amari a matsayin abin baƙin ciki sosai, ya kuma mika ta’aziyyasa ga iyalan wadanda lamarin ya shafa.
An kuma bayar da umarnin gudanar da binciken gaggawa don gano musabbabin gobarar da kuma wanda ya dace a ɗauki mataki a kansa.
News Translation in English Language.
Fire at Indian Hospital Kills 10 Patients.
A fire broke out in the Intensive Care Unit (ICU) of SCB Medical College and Hospital in Cuttack, located in the eastern Indian state of Odisha, on Monday morning.
Local health authorities reported that 10 people died as hospital staff attempted to move patients to safer areas away from the blaze. At the time of the fire, 23 patients were in the ICU.
Preliminary investigations suggest that an electrical fault is the most likely cause of the fire, a common risk in buildings where wiring and electrical systems are poorly maintained.
The hospital confirmed that staff and security personnel were injured while rescuing patients.
Indian Prime Minister Narendra Modi described the incident as “deeply tragic” and extended condolences to the families of those affected.
A rapid inquiry has been ordered to determine the cause of the fire and identify those responsible for any lapses.

0 Comments:
Post a Comment