Mayakan ƙungiyar Boko Haram sun sake kai hari wani hari a sansanin sojojin Najeriya dake jihar Borno, lamarin da ya ƙara nuna yadda hare-haren ‘yan ta’adda ke ƙaruwa a yankin Arewa maso Gabas na ƙasar.
Rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne a wani sansanin soja da ke Ajilari, wani yanki da ke kusa da birnin Maiduguri, babban birnin jihar. Harin ya faru ne da sanyin safiyar Litinin inda aka ce an ji ƙarar harbe-harbe da fashe-fashe a yankin.
Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa mayakan sun farmaki sansanin sojojin ne da makamai masu karfi, lamarin da ya janyo arangama mai zafi tsakanin su da sojojin Nigeriya.
Sai dai zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a fitar da cikakken bayani kan yawan waɗanda suka mutu ko suka jikkata ba sakamakon harin. Haka kuma, hukumomin tsaro ba su yi cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru ba.
Wannan sabon harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar ƙarin hare-haren ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas, inda ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi ke kai hare-hare kan sansanonin sojoji da kuma wasu al’ummomi.
Masana harkokin tsaro na cewa irin waɗannan hare-hare na nuna cewa har yanzu akwai buƙatar ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ta’addanci domin dawo da cikakkiyar tsaro a yankin.
_4.webp)
0 Comments:
Post a Comment