Akalla mutane 13 ne suka rasa rayukansu sakamakon wasu sabbin hare-haren sama da sojojin Israi'la suka kai a yankin zirin Gaza, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Majiyoyin lafiya a yankin sun ce daga cikin wadanda suka mutu akwai yara biyu da kuma wata mata mai juna biyu, yayin da wasu mutane da dama suka jikkata sakamakon tashin bama-bamai da suka ruguza wasu gidajen fararen hula.
Rahotanni sun nuna cewa hare-haren sun afku ne a wasu unguwannin da fararen hula ke zaune, lamarin da ya haddasa lalacewar gidaje da sauran kadarori, tare da jefa al’ummar yankin cikin halin firgici.
Wannan sabon harin na zuwa ne a daidai lokacin da rikici tsakanin Isra’ila da kungiyoyin Falasdinawa ke ci gaba da tsananta a yankin, inda hare-hare da ramuwar gayya ke kara janyo asarar rayuka da barnar ababen more rayuwa.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama da wasu kasashe sun sake yin kira ga bangarorin da ke rikicin da su dakatar da hare-haren da ke shafar fararen hula, musamman mata da yara, tare da bukatar a kara kokarin diflomasiyya domin kawo karshen rikicin da ke ci gaba da addabar yankin.

0 Comments:
Post a Comment