Gwamnatin Sifaniya ta bayyana cewa ba za ta ba da izinin amfani da tashoshin Jiragen sojan ta a Rota da Morón ba don kai hare-hare kan Iran cikin rikicin da Amurka da Isra’ila ke jagoranta.
Shugaban gwamnati Pedro Sánchez ya yi kakkausan Allah wadai da ayyukan sojan da Amurka da Isra’ila suka fara, yana mai cewa sun saba wa dokokin kasa da kasa kuma suna iya haifar da rashin kwanciyar hankali a duniya.
Ministan harkokin wajen Sifaniya, José Manuel Albares, ya jaddada cewa ba za a yi amfani da waɗannan Sansanonin soji don ayyukan da ba su cikin yarjejeniyar da aka cimma ƙarƙashin Doka ta Majalisar Ɗinkin Duniya ba, kuma gwamnatin tana dagewa kan kiyaye ‘yancin kanta.
Sakamakon wannan mataki, wasu jiragen Amurka guda goma sha biyar sun bar tashoshin Rota da Morón zuwa wasu wurare, ciki har da tashar sojan Ramstein a Jamus.
Hakan ya bambanta da matsayin ƙasashen Turai da dama, inda wasu kamar Birtaniya da Faransa suka amince da bayar da izini a wasu yanayi na “kare kai”, yayin da Sifaniya ta tsaya kan neman zaman lafiya da warware rikice-rikice ta hanyar diplomasiyya.
Tags
Labarai
