Mabiya Darikar Qadiriyya a Kano Sun Yi Sallar Jana’iza (Salatul Gha’ib) Ga Ayatollah Khamenei.


Wasu mabiya Darikar Qadiriyya a jihar Kano sun gudanar da sallar jana’iza ta (Salatul Gha’ib) domin nuna alhini da girmamawa ga Jagoran Juyin Juya Halin ƙasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da sallar ne bayan bazuwar labaran mutuwarsa, inda mabiya darikar suka bayyana kaduwarsu tare da addu’o’in neman rahamar Allah ga mamacin. Mahalarta taron sun jaddada cewa matakin da suka dauka na nuna alaka ta addini da kuma goyon bayan jagoran Musulunci da suke dauka a matsayin abin koyi.

Wani daga cikin jagororin darikar ya ce irin wannan salla ta Salatul ga'ib abu ne da addinin Musulunci ya tanada domin girmama manyan mutane da suka rasu a kasashen waje, musamman idan labarin mutuwarsu ya shafi al’ummar Musulmi baki daya.

Darikar Qadiriyya na daga cikin manyan darikun Sufaye da ke da karfi a Kano da sauran sassan arewacin Najeriya, inda take taka rawa a harkokin addini da zamantakewa.

An ruwaito cewa taron ya gudana cikin kwanciyar hankali, ba tare da wata tangarda ba, yayin da jami’an tsaro suka tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form