Dubban masu zanga-zanga sun yi rikici da ‘yan sanda a babban birnin Tirana yayin da suka fita neman a sauke Firaminista Edi Rama, sakamakon zarge-zargen cin hanci da rashawa a gwamnatin kasar.
Zanga-zangar ta karu bayan da Mataimakiyar Firaminista, Belinda Balluku, wadda ke da kusanci da Rama, ta fuskanci tuhume-tuhume na cin hanci da rashawa dangane da karbe ayyukan gwamnati ba bisa ka’ida ba.
Balluku ta musanta zargin, amma an dakatar da ita daga mukaminta yayin da kotu ke neman a cire mata kariyar doka don a gurfanar da ita.
‘Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da ruwan famfo don tarwatsa masu zanga-zangar, inda wasu aka kama su.
Masu zanga-zangar sun hada da magoya bayan jam’iyyar adawa ta Democratic Party, karkashin jagorancin Sali Berisha, wadanda ke rera kalaman kiran Rama ya sauka daga mukaminsa.
Zanga-zangar tana zuwa ne a daidai lokacin da Albania ke neman shiga kungiyar Tarayyar Turai (EU) nan da 2030, yayin da kungiyar EU ke jaddada muhimmancin yaki da cin hanci da rashawa da karfafa dokokin kasa a matsayin sharadi.
Rikicin siyasa a Albania ya nuna yadda rarrabuwar kawuna cikin jam’iyyu da rashin amincewa da shugabanci ke haifar da tashin hankali a kasar, yayin da gwamnatin Rama ke ci gaba da rike rinjayen majalisar ƙasar.
News translation in English Language.
Clashes Erupt in Albania as Protesters Demand Prime Minister Edi Rama’s Resignation.
Violent clashes broke out in the Albanian capital on Friday as thousands of protesters took to the streets demanding the resignation of Prime Minister Edi Rama, amid mounting anger over corruption allegations within the government.
Demonstrators confronted police near key government buildings in Tirana, with security forces firing tear gas and using water cannons to disperse the crowds. Several people were reported arrested during the unrest.
The protests were triggered by corruption charges against Deputy Prime Minister Belinda Balluku, a close ally of Rama, who has been accused of interfering in public procurement contracts. Balluku has denied the allegations but was suspended from office as prosecutors pursue the case.
Many of the protesters are supporters of the opposition Democratic Party, led by former prime minister Sali Berisha, who has repeatedly accused the government of widespread corruption and called for Rama to step down.
The political turmoil comes at a sensitive time for Albania, which is seeking to advance its bid for membership in the European Union. EU officials have stressed that strengthening the rule of law and tackling corruption are key conditions for accession.
Despite the unrest, Rama’s ruling Socialist Party maintains a strong majority in parliament, while authorities insist that the legal process against Balluku should be allowed to proceed without political interference.
Tags
Labarai
