An fara kada kuri’a a wasu runfunar Zabe a sassan babban birnin Tarayyar Abuja, a zaben Kananan Hukumomi, inda jami’an hukumar zaɓe na Ƙasa, INEC da wakilan jam’iyyu ke sa ido a wurin.
Hakan na zuwa ne yayin da masu kada kuri’a ke shiga rumfunan zabe domin gudanar da zabukan su cikin lumana, tare da tabbatar da cewa an bi ka’idojin zabe yadda ya kamata.
Masu sa ido sun tabbatar da cewa dukkan kayan aikin zabe sun iso Rumfunan zaɓen kuma suna aiki yadda ya kamata, yayin da jami’an tsaro ke tabbatar da kiyaye zaman lafiya a wajen zabe.
Tags
Labarai
