Shugaban ƙasar Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, ya bayyana cewa ya kamata a yi wa tsohon shugaban Venezuela, Nicolás Maduro, shari’a a cikin Venezuela ne, ba a Amurka ba.
Lula ya yi wannan bayani ne yayin wata hira a gefen wani taron ƙasa da ƙasa da aka gudanar a Indiya, inda ya jaddada muhimmancin ikon ƙasa da ‘yancin shari’a.
A cewarsa, ba daidai ba ne wata ƙasa ta kama shugaba ko tsohon shugaba ta kai shi waje domin shari’a, musamman ma idan abin ya shafi makwabtan yankin Amurka ta Kudu.
Shugaban na Brazil ya yi gargadin cewa irin wannan mataki na iya zama mummunar jari-hujja a hulɗar ƙasashen duniya, yana iya raunana dokokin ƙasa da ƙa’idojin diflomasiyya.
Maganganun sun biyo bayan kama Maduro a farkon shekarar 2026, inda aka kai shi New York domin fuskantar tuhuma kan safarar miyagun ƙwayoyi da wasu laifuka. Lula ya kuma sake nanata burin Brazil na ganin demokiraɗiyya ta dawo a Venezuela, tare da kiran a mutunta ka’idojin dokar ƙasa da ƙasa.
News Translation in English Language.
Brazil’s president, Luiz Inácio Lula da Silva, has said that former Venezuelan leader Nicolás Maduro should face trial in Venezuela, rather than in the United States.
Lula made the remarks during an interview on the sidelines of an international event in India, stressing the importance of national sovereignty and domestic judicial authority. He said it was unacceptable for a foreign country to detain a current or former head of state and prosecute them abroad, particularly within the South American region.
The Brazilian leader warned that such actions could set a dangerous precedent in international relations, undermining established legal norms and diplomatic principles.
His comments follow the detention of Maduro earlier in 2026, when he was taken to New York to face charges related to drug trafficking and other alleged crimes. Lula reiterated Brazil’s position in favour of seeing democracy restored in Venezuela, while calling for respect for international law and due process.
Tags
Labarai
