Akalla mutane 50 ne suka rasa rayukansu bayan wasu ’yan bindiga dauke da makamai a kan babura, sun kai wani mummunan hari kan al’umman garin Tungan Dutse, da ke cikin ƙaramar hukumar Bukkuyum, a Jihar Zamfara.
Rahotanni daga mazauna yankin da kuma wakilan gwamnati sun bayyana cewa maharan sun kai harin ne cikin dare, inda suka rika kutsawa cikin gidaje suna harbe-harbe, tare da kona gidaje da kadarori.
Har ila yau, an ce mata da yara da dama an sace su, yayin da ake ci gaba da tantance adadin wadanda abin ya shafa.
Wani dan majalisar yankin ya bayyana cewa an riga an sanar da jami’an tsaro game da motsin ’yan bindiga kafin harin, amma ba a dauki matakin gaggawa ba domin dakile afkuwar lamarin.
Masana tsaro sun ce harin na daga cikin yawaitar matsalar rashin tsaro a yankunan arewa maso yammacin Najeriya, inda ’yan bindiga da gungun masu aikata laifuka ke yawan kai hare-haren sace-sace da kisan jama’a.
Gwamnati ta ce tana ci gaba da kokarin karfafa matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, yayin da jama’ar yankin ke neman daukar mataki mai karfi don kawo karshen ta’addancin da ya addabi yankin.
Tags
Labarai
