Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke mutane tara (9) saboda cin abinci a fili yayin da ake gudanar da azumin watan Ramadan.
Rahotanni sun nuna cewa wadanda aka cafke sun bayyana wa jami’an Hisbah cewa basu san lokacin fara Azumin Ramadan yayi ba.
Hukumar ta bayyana cewa matakin cafke mutanen an dauke shi ne don ilimantarwa — domin su fahimci muhimmancin azumi da sallah, da karatun Al-Qur’ani.
Kano na daga cikin jihohi 12 a arewacin Najeriya da suka kafa dokokin Shari’a tare da tsarin shari’a na musamman da ke kula da addini, ciki har da bin azumi na watan Ramadan, wanda wajibi ne ga kowane musulmi baligi.
Tags
Labarai
