‘Yan ta’adda sun kashe musulmai 34 masu azumi a wani sabon hari da suka kai jihar Kebbi.

‘Yan ta’adda sun kashe musulmai 34 masu azumi a wani sabon hari da suka kai jihar Kebbi.

Akalla mutane 34 ne suka rasa rayukansu da azumi a bakinsu a wani hari da ‘yan ta’adda suka kai a wasu ƙauyuka na Jihar Kebbi, cikin ƙaramar hukumar Arewa-dandi a ranar Laraba, kamar yadda jami’an tsaro suka sanar. 

Rahotanni sun nuna cewa maharan Lakurawa ne suka kai farmaki a garuruwan da suka haɗa da Mamunu da Awasaka da Masama da Tungan Tsoho da Makangara da Kanzo da Gorun Naidal da Dan Mai Ago, suna harbe‑harben da ya sa mazauna suka gudu domin neman mafaka. 

Jami’an tsaro sun ce an samu mutuwar mutane 16 a Mamunu, sai 5 a Awashaka da 3 a Masama, da wasu mutanen biyu‑biyu a sauran ƙauyukan da abin ya shafa. 
An ce harin ya tilasta mazauna barin gidajensu yayin da maharan suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi. 

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kebbi ta tabbatar da afkuwar lamarin, inda kakakinta, SP Bashir Usman, ya ce jami’an tsaro sun tura ƙarin sojoji da ‘yan sanda domin dawo da zaman lafiya da taimakawa waɗanda abin ya shafa, da kuma hanawa maharan tserewa. 

A jawabin gwamnati, Mashawarancin Gwamnan jihar kan Harkokin Sadarwa da Tsare‑tsare, Alhaji Abdullahi Idris Zuru, ya bayyana harin a matsayin wani abin ƙiyayya da rashin tausayi, ya kuma yi alƙawarin cewa gwamnatin jihar za ta yi aiki tare da rundunar soji don kawar da barazanar tsaro. 
Ya ce waɗanda suka tsira za su sami tallafi nan da nan daga gwamnati. 

Har yanzu hukumomi na ci gaba da gudanar da bincike da farautar waɗanda ake zargi, yayin da al’ummar yankin ke cikin bakin ciki kan asarar rayukan mutanen da suka faru a lokacin azumi. 

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form