Gwamnatin Venezuela ta yi afuwa ga ’yan siyasan ƙasar su 379 da ke kulle a gidajen yarin ƙasar.

Gwamnatin Venezuela ta yi afuwa ga ’yan siyasan ƙasar su 379 da ke kulle a gidajen yarin ƙasar.

Gwamnatin Venezuela ta yi afuwa ga ’yan siyasa 379 da ake tsare da su, a matakin da ake ganin zai rage rikicin siyasa a kasar. 
Wannan mataki ya biyo bayan dokar afuwa ne da gwamnatin wucin gadi ta amince da ita, inda ake sa ran zai bai wa wadanda aka tsare ’yancin fita daga gidan yari nan ba da jimawa ba.

Jorge Arreaza, jami’in gwamnati, ya bayyana cewa an tsara sakin wadannan mutanen nan da dare ko gobe, yayin da kotunan kasar za su tabbatar da aiwatar da wannan mataki. 
Sai dai shugabannin ’yan adawa sun nuna damuwa cewa dokar ba ta shafi wasu wadanda suke goyon bayan ayyukan adawa ba, musamman wadanda ake zargin da tada tarzoma ko kuma ayyukan soji.

Ana ganin wannan mataki zai iya rage tashin hankali a kasar, duk da cewa har yanzu akwai wadanda ke tsare saboda laifukan da suka shafi “ta’addanci” da sauran manyan laifuka.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form