Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa yarjejeniya tsakanin kasarsa da Amurka na iya samuwa cikin sauƙi, muddin aka bai wa diflomasiyya cikakkiyar muhimmanci.
Araghchi ya yi wannan bayani ne a gabanin sabon zagayen tattaunawa da ake sa ran za a gudanar a birnin Geneva na ƙasar Switzerland, inda ya jaddada cewa Iran na ganin wannan lokaci a matsayin wata babbar dama ta tarihi domin cimma yarjejeniya da za ta amfanar da ɓangarorin biyu.
Ministan ya ce Iran ba ta da niyyar kera makamin nukiliya, yana mai nanata cewa burin ƙasar shi ne samun ‘yancin amfani da fasahar nukiliya ta hanyoyin zaman lafiya kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.
Ya kuma ƙara da cewa duk wata yarjejeniya dole ne ta ginu bisa mutunta juna da tattaunawa mai ma’ana.
Rahotanni sun nuna cewa tattaunawar na gudana ne a wani yanayi da ke cike da ƙalubale, musamman ganin yadda Amurka ta ƙara yawan dakarunta a yankin gabas ta tsakiya, tare da yin barazanar ɗaukar matakan soja idan aka gaza cimma matsaya ta diflomasiyya.
Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa sakon Iran na nuni da buɗe ƙofa ga sulhu, amma sun ce nasarar tattaunawar za ta dogara ne kan yadda ɓangarorin biyu za su yi sassauci da kuma fifita diflomasiyya a kan barazana da amfani da ƙarfi.
News Translation in English Language.
Iran Says Deal With US Is Possible If Diplomacy Takes Priority
Tehran / Geneva – Iran’s Foreign Minister has said that an agreement between Iran and the United States is within reach, provided diplomacy is given priority over pressure and threats.
Speaking ahead of a new round of talks expected to take place in Geneva, Foreign Minister Abbas Araghchi described the current moment as a historic opportunity to reach a deal that could benefit both sides.
He reiterated that Iran has no intention of developing nuclear weapons, stressing that the country is only seeking its legitimate right to use nuclear technology for peaceful purposes under international law.
The talks come amid heightened regional tensions, with the United States increasing its military presence in the region and warning that it may consider force if negotiations fail.
Political analysts say Iran’s remarks signal openness to compromise, but caution that progress will depend on whether both sides choose dialogue over confrontation.
Tags
Labarai
