Mbappé ba zai buga wasan Real Madrid da Benfica ba sakamakon raunin da ya samu.

Mbappé ba zai buga wasan Real Madrid da Benfica ba sakamakon raunin da ya samu.

Tauraron dan wasan Real Madrid, Kylian Mbappé ba zai buga wa Real Madrid wasan Gasar Zakarun Turai na UEFA Champions League da Benfica ba, sakamakon raunin gwiwa da ke damunsa.

Rahotanni sun bayyana cewa Mbappé ya kasa kammala atisayen da kungiyar ta yi a ranar Litinin, lamarin da ya sa masu horaswa da likitocin kulob din suka yanke shawarar hutar da shi domin kauce wa kara tsananta raunin.

Real Madrid na shirin karɓar bakuncin Benfica a wasan zagaye na biyu na UEFA Champions League, inda kungiyar ta Sifaniya ke da tagomashin nasara 1–0 daga wasan farko. 
Rashin Mbappé na iya zama babban gibi ga Real Madrid, kasancewarsa daya daga cikin manyan ‘yan wasan da ke jan ragamar cin kwallaye a kakar bana.

Rahotanni daga kulob din sun nuna cewa ana sa ran Mbappé zai murmure nan ba da jimawa ba, kuma ba za a yi gaggawar dawo da shi fili ba har sai an tabbatar da cikakken lafiyarsa.

Masu kallo da masoya kwallon kafa na sa ido domin ganin yadda Real Madrid za ta tsara wasanta ba tare da tauraron nata ba, yayin da Benfica ke fatan yin anfani da wannan damar domin juyar da akalar fafatawar.

News Translation in English Language.

Real Madrid Faces Benfica Without Mbappé.

Madrid, Spain — Kylian Mbappé will miss Real Madrid’s Champions League return leg against Benfica due to a lingering knee problem.

The French forward’s withdrawal follows a training session cut short after experiencing discomfort, highlighting ongoing concerns over his fitness. Real Madrid currently leads 1–0 from the first-leg clash and will aim to maintain the advantage at home.

His absence may force coach Álvaro Arbeloa to rethink attacking strategies, as Mbappé has been a central figure in the team’s offensive play this season. 
Benfica, meanwhile, will attempt to capitalize on Madrid’s weakened lineup to overturn the deficit.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form