Donald Trump Ya Gabatar da Jawabin “hadin Kan ƙasa” na 2026, inda ya kare Manufofinsa a gaban majalisar dokokin ƙasar.

Donald Trump Ya Gabatar da Jawabin “hadin Kan ƙasa” na 2026, inda ya kare Manufofinsa a gaban majalisar dokokin ƙasar.

Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya gabatar da jawabin hadin Kan ƙasa na shekarar 2026 a gaban zaman majalisar dokokin ƙasar a birnin Washington, D.C., inda ya bayyana manyan manufofin gwamnatinsa tare da kare matakan da ya dauka a fannin tattalin arziki da tsaron ƙasa.

A cikin jawabin, Trump ya ce gwamnatinsa ta samu ci gaba wajen samar da ayyukan yi da farfaɗo da masana’antu da kuma ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar. 

Ya jaddada cewa manufofinsa na kasuwanci da haraji suna da nufin kare muradun ‘yan Amurka da bunƙasa masana’antar cikin gida.

Shugaban ƙasar ya kuma tabo batutuwan siyasar duniya, inda ya ambaci dangantakar Amurka da ƙasashen waje, musamman a Gabas ta Tsakiya, tare da nuna cewa gwamnatinsa na neman cimma tsaro da zaman lafiya ta hanyar diplomasiyya da ƙarfi idan bukata ta taso.

Sai dai jawabin ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da rarrabuwar kai a siyasar cikin gida, inda wasu ‘yan adawa suka nuna rashin amincewa da manufofin shugaban ƙasar, wasu ma suka kaurace wa zaman a matsayin nuna adawa.

Masana harkokin siyasa na ganin jawabin na 2026 a matsayin wata muhimmiyar hanya da Trump ya bi domin isar da saƙonsa ga ‘yan ƙasa, musamman gabanin manyan zaɓukan siyasa masu zuwa a Amurka.

News Translation in English Language.

Trump Delivers 2026 State of the Union, Emphasises Economy and National Security.

Washington, D.C. — United States President Donald Trump on Monday delivered the 2026 State of the Union address before a joint session of the United States Congress, outlining his administration’s priorities with a strong focus on economic performance and national security.

In his address at the Capitol in Washington, D.C., President Trump said his government had recorded significant progress in job creation, industrial revival and overall economic growth. He defended his trade and tariff policies, describing them as necessary measures to protect American industries and reduce dependence on foreign imports.

The president also spoke on foreign policy, noting that the United States would continue to safeguard its interests globally while pursuing peace through diplomacy and strategic partnerships. He stressed that national security would remain a central pillar of his administration’s agenda.

However, the address came against the backdrop of deep political divisions, with several opposition lawmakers expressing dissatisfaction with the president’s policies and some staging symbolic protests during the session.

Political analysts say the 2026 State of the Union served as a key platform for President Trump to restate his policy direction and rally public support ahead of major political contests later in the year.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form