Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta cafke wani mutum mai suna Gafaru Rasaki bisa zarginsa da tono gawarwakin mutane daga makabarta da ke garin Sagamu tare da samun wasu kawuna guda hudu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Oluseyi Babaseyi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Alhamis a Abeokuta, inda ya ce jami’an ‘yan sanda na shiyyar Shakura da ke Sagamu sun kama wanda ake zargin a ranar 21 ga watan Janairu, 2026.
“A ranar 21 ga Janairu, 2026, jami’an sashin Shakura sun kama wani Gafaru Rasaki da kawuna hudu na mutane.
“Bayan an yi masa tambayoyi da cikakken bincike, an gano cewa wanda ake zargin ya tono gawarwakin mutanen ne ba bisa ka’ida ba daga makabarta.
"Wannan wani aiki ne da ya nuna rashin mutunta gawarwaki da kuma keta doka," in ji Babaseyi
Babaseyi ya ce an ajiye kawunan a inda ya dace, inda ya kara da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu idan aka kammala bincike.
Kakakin ‘yan sandan ya sake jaddada aniyar rundunar na kare lafiyar jama’a tare da gargadin cewa duk wanda ke da hannu wajen tozarta gawar dan Adam zai fuskanci cikakken nauyin doka.
Tags
Labarai
