'Yan bindiga sun sako ragowar masu ibada da suka yi garkuwa da su a makon da ya gabata a jihar Kaduna.

'Yan bindiga sun sako ragowar masu ibada da suka yi garkuwa da su a makon da ya gabata a jihar Kaduna.

'Yan bindiga sun sako ragowar masu ibada da suka yi garkuwa da su a makon da ya gabata a jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce ‘yan bindiga sun sako sauran masu ibada da suka yi garkuwa da su a wani hari da suka kai a ranar Lahadin da ta gabata a coci-coci a yankin Kurmin Wali da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Harin dai ya faru ne a lokacin da wasu mutane dauke da makamai suka kutsa kai cikin wasu majami'u guda uku a cikin garin a lokacin da ake gudanar da ibada, inda suka yi ta harbe-harbe don sanya tsoro kafin su yi awon gaba da masu ibadan tare da kai su cikin dazuzzuka.

Idan ba manta ba dai, an yi garkuwa da mutane akalla 177 masu ibada a yayin harin. 
Daga baya an samu Rahotan cewa kimanin masu ibada 80 ne suka tsere yayin da aka kai su cikin daji inda daga bisani suka fake a kauyukan da ke makwabtaka da su.

Da yake tabbatar da hakan a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a yau ranar Alhamis, Hakimin kauyen Kurmin Wali, Ishaku Dan’azumi, ya ce da safiyar Talata ya samu labarin cewa an sako masu ibadar da aka sace.

"Na samu labarin sakin su da safiyar yau, a halin yanzu suna tare da gwamnati a Kaduna," in ji shi, ya kara da cewa ba zai iya bayar da karin bayani ba a halin yanzu.

Da aka tambaye shi ko an bayar da kudin fansa ko babura da ake zargin ‘yan fashin ne suka nema kafin a sako su, Dan’azumi ya ce bai iya tabbatar da hakan ba, inda ya ce yana shirin tafiya Kaduna domin ganawa da wadanda lamarin ya shafa.

Shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen jihar Kaduna, Rabaran Ma’aji Caleb, shi ma ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form