Kotu ta yankewa tsohon manajan daraktan bankin shigo da kaya na Najeriya (NEXIM) hukuncin daurin shekaru 490 a gidan yari bisa Almundahanar N2.4bn.


Kotu ta yankewa tsohon manajan daraktan bankin shigo da kaya na Najeriya (NEXIM) hukuncin daurin shekaru 490 a gidan yari bisa Almundahanar N2.4bn.

Wata babbar kotu a babban birnin tarayya Abuja ta yankewa tsohon manajan daraktan bankin shigo da kaya na Najeriya (NEXIM), Robert Orya, daurin shekaru 490 a gidan yari bisa samunsa da laifin almundahanar Naira biliyan 2.4.

A ranar Alhamis ne mai shari’a F.E. Messiri ta yanke wa Orya hukuncin daurin shekaru 10 a kan kowanne daga cikin tuhume-tuhume 49 da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta shigar a kansa, tare da zartar da hukuncin a Lokaci guda.

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta shigar da karar ne ta hannun lauyanta Samuel Ugwuegbulem.

Orya ya rike mukamin Manajan Darakta na Bankin NEXIM daga shekara ta 2009 zuwa 2016, inda a lokacin ne aka yaba masa da kokarin sauya ayyukansa bankin bayan kalubalen kudi a baya.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form