’Yan Sanda Sun Kama Mutane Shida da Ake Zargi da Satar Motoci a Kano.

’Yan Sanda Sun Kama Mutane Shida da Ake Zargi da Satar Motoci a Kano.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama mutane shida da ake zargi suna cikin wata ƙungiyar satar motoci, tare da kwato motoci uku da ake zargin an sace.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da kamen a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya bayyana cewa an samu nasarar ne sakamakon tsauraran matakan tsaro da rundunar ke aiwatarwa a faɗin Jihar Kano.

A cewarsa, bincike na ci gaba da gudana domin gano sauran mambobin ƙungiyar da kuma tabbatar da an gurfanar da waɗanda aka kama a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Rundunar ta kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro domin taimakawa wajen yaƙi da laifuka, musamman satar motoci, domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.

News Translation in English Language.

Police Bust Car-Theft Ring in Kano, Arrest Six and Recover Three Vehicles.

Kano – The Kano State Police Command has dismantled a suspected car-theft syndicate with the arrest of six suspects and the recovery of three stolen vehicles during coordinated security operations across the state.

According to the Command’s spokesperson, Abdullahi Haruna, the arrests were made following actionable intelligence and sustained patrols aimed at curbing vehicle-related crimes. He said preliminary investigations indicate that the suspects are linked to a network responsible for stealing and reselling vehicles within and beyond the state.

Haruna disclosed that further investigations are underway to identify additional accomplices and recover more stolen assets. He assured that the suspects currently in custody will be arraigned in court once investigations are concluded.

The police reiterated their commitment to protecting lives and property and called on residents of Kano State to continue supporting law enforcement agencies with timely and credible information to enhance public safety.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form