Jami’an tsaron dake gadin gidan hutun Shugaban Amurka sun kashe wani mutum dauke da makami bayan da ya kutsa kai cikin gidan hutun, Mar-a-Lago, mallakin shugaban Amurka, Donald Trump, a safiyar Lahadi a jihar Florida.
A cewar bayanan hukumomi, lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:30 na dare, lokacin da jami’an tsaro suka gano mutumin yana shiga yankin da ke karkashin tsauraran matakan tsaro. Rahotanni sun nuna cewa mutumin yana dauke da bindiga da kuma galan man fetur lokacin da aka tare shi.
An bayyana cewa jami’an tsaron sun umurce shi da ya ajiye makamansa.
Duk da cewa ya sauke galan din man fetur, sai dai rahotanni sun ce ya daga bindigar hannunsa, lamarin da ya tilasta wa jami’an tsaron bude masa wuta, wanda ya yi sanadin mutuwarsa nan take.
Hukumomi sun tabbatar da cewa babu wani jami’in tsaro da ya samu rauni a yayin afkuwar lamarin. Haka kuma, an ce Donald Trump bai kasance a gidan hutun na Mar-a-Lago ba a lokacin da lamarin ya faru.
Ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano dalilin da ya sa mutumin ya kutsa cikin yankin tsaron, yayin da hukumomin tsaro ke kira ga jama’a da su bayar da duk wani bayani ko faifan bidiyo da zai taimaka wajen kammala binciken.
News Translation in English Language.
Armed Intruder Killed After Breaching Security at Trump’s Mar-a-Lago Estate
Palm Beach, Florida — Agents of the United States Secret Service shot and killed an armed man after he breached the secure perimeter of Mar-a-Lago, the Florida resort owned by former US President Donald Trump, early Sunday morning.
According to official statements, the incident occurred around 1:30 a.m. when security personnel detected a man unlawfully entering the highly restricted area. The suspect was reportedly carrying a firearm and a container believed to contain gasoline.
Authorities said the man was ordered to drop his weapons. While he reportedly put down the container, he raised the firearm, prompting Secret Service agents, with support from local law enforcement, to open fire. The suspect was pronounced dead at the scene.
No injuries were reported among security personnel. Officials confirmed that Donald Trump was not present at the Mar-a-Lago property at the time of the incident.
Investigations are ongoing to determine the suspect’s motive, as federal and local authorities continue to review security footage and gather additional information.
Tags
Labarai
