Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta cafke wasu mutane shida bisa zarginsu da hannu a satar adaidaita sahu da kuma sayar da kayan sata a cikin jihar.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, bayan korafin da Ayuba Muhammad ya shigar cewa an sace masa adaidaita sahu a unguwar Panshekara a ranar 24 ga Janairu, 2026.
A cewar Kiyawa, an kama wadanda ake zargin ne bisa laifukan hada baki domin aikata laifi, sata da kuma sayen kayan sata.
Ya bayyana sunayen biyar daga cikin wadanda ake zargin da suka hada da Salim Zakari (shekara 20), Faruk Abubakar (shekara 17), Yusuf Garba (shekara 20), Mastur Shehu (shekara 19) da Safiyanu Suleiman (shekara 23). Na shida kuwa shi ne Umar Bello Dahiru (shekara 24), wanda ake zargi da sayen adaidaita sahun da aka sace.
Sanarwar ta ce an sayar da adaidaita sahun da aka sace, mai lambar rajista BBR 195 CB da lambar KAROTA NMC 1229, wanda kudinsa ya kai naira miliyan 3.5, ga Umar Bello Dahiru.
Binciken ’yan sanda ya kuma danganta wadanda ake zargin da wata satar adaidaita sahu a unguwar Yankusa.
Kiyawa ya kara da cewa sahihin bincike ya kai ga cafke Dahiru, inda aka kwato adaidaita sahu biyu daga hannunsa. Ana zarginsa da amsa laifin cewa ya sayi kayan ne yana sane da cewa an sace su.
Haka kuma, rundunar ta ce an kwato doki da kudinsa ya kai naira 800,000, wanda ake zargin an saya shi ne da kudaden da aka samu daga laifin.
’Yan sanda sun tabbatar da cewa an mayar da adaidaita sahun da aka kwato ga masu su, wato Ayuba Muhammad da Abdullahi Adamu, tare da jaddada cewa bincike na ci gaba.
Rundunar ta kuma sake nanata kudurinta na yaki da laifuka ta hanyar amfani da sahihan bayanan sirri domin tabbatar da tsaro a jihar.
Tags
Labarai
